Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Abigail Marshall-Katung Ta Kafa Tarihi A Matsayin Magajiyar Garin Leeds


Abigail Marshall-Katung
Abigail Marshall-Katung

Za ta kafa tarihi a watan Mayu, bayan da abokan aikinta baki danayansu suka zabe ta a matsayin Magajiyar garin Leeds a Burtaniya.

An zabi Abigail Marshall-Katung a matsayin Magajiyar garin Leeds na 130 - kuma za ta kasance mace ta farko daga Afirka da ke rike da mukamin mai daraja.

'Yar shekaru 48 da haihuwa ta ce tana matukar "girmama da kaskantar da kai" don karbar aikin, wanda ya zo bayan shekaru biyar na hidima a Majalisar Birnin Leeds.

Za ta kafa tarihi a watan Mayu, bayan da abokan aikinta baki danayansu suka zabe ta a matsayin.

An haifi Abigail a Najeriya ne kafin ta kaura zuwa Leeds inda ta karanci harkokin siyasa a shekarar 2000.

A lokacin ne ta gano irin son da take yi wa garin wanda hakan ya sa ta koma karamar hukumar.

Ta sha alwashin "ci gaba da yakin neman daidaito da adalci na zamantakewa" a matsayin magajiyar gari, wanda ta fara tun lokacin da aka zabe ta don wakiltar Little London da Woodhouse a 2019.

Mijinta Sunday Marshall-Katung shi ma dan siyasa ne, wanda ya zama Sanata a Najeriya.

Abigail za ta karbi mulki daga Al Garthwaite, dan majalisar Labour na Headingley da Hyde Park ward, wanda aka zabe shi a matsayin magajin garin Leeds a bara.

Ta bi sahun Eileen Taylor, wacce ta zama bakar fata ta farko da ta rike mukamin magajin gari a shekarar 2019.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG