Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashe Da Dama Sun Dakatar Da Bayar Da Tallafi Ga Hukumar Majalisar Dinkin Duniya A Gaza


Shugaban hukumar UNRWA, Philippe Lazzarini
Shugaban hukumar UNRWA, Philippe Lazzarini

Manyan kasashe masu ba da agaji da dama sun ce za su dakatar da bayar da kudade ga hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Falasdinu ta Majalisar Dinkin Duniya, biyo bayan zargin da Isra'ila ta yi na cewa ma'aikatanta na da hannu a harin da kungiyar Hamas ta kai ranar 7 ga watan Oktoban 2023.

Hukumar ta UNRWA ta kori mutane da dama daga aiki tare da yin alkawarin gudanar da cikakken bincike kan ikirarin da ba a fayyace ba, yayin da Isra'ila ta sha alwashin dakatar da ayyukan hukumar a Gaza bayan yakin.

Shugaban hukumar UNRWA, Philippe Lazzarini, ya yi alƙawarin hukunta duk wani ma'aikaci da aka samu da hannu a "ayyukan ta'addanci".

Shugaban Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres shi ma ya yi alƙawarin yin binciken gaggawa mai zaman kansa akan UNRWA, amma kuma ya roki ƙasashe masu ba da gudummowa da su “ba da tabbacin ganin ayyukan hukumar sun ci gaba, saboda al’umar yankin da ke cikin matsanancin hali.

Amurka ta fada a ranar Juma’a cewa ta dakatar da bayar da kudade ga hukumar ta Majalisar Dinkin Duniyar, matakin da wasu kasashe da dama suka bi sahu, kamar Burtaniyya, Jamus, Faransa, Switzerland, Canada, Finland, Japan, Italiya, Netherlands da Norway.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG