Bangarorin biyu sun yi alkawarin yin aiki don tabbatar da an yi zaben gaskiya da adalci a shekarar 2024.
Amurka ta yaba da yarjejeniyar, kuma jim kadan bayan haka ta sanar da cewa za ta dage takunkumin da ta kakaba wa masana'antar mai da iskar gas ta Venezuela na wani dan lokaci. An samu ci gaba a adangantaka tsakanin Amurka da Venezuela a cikin watan Disamba, lokacin da aka yi musayar fursunoni tsakanin kasashen biyu a matsayin wata yarjejeniyar da ta kuma kunshi alkawarin da gwamnatin Maduro ta yi na sakin fursunonin siyasar Venezuela sama da ashirin.
Sai dai a yanzu, Amurka "ta damu matuka kan bayar da umarnin kame da kuma tsare mutane akalla 33 'yan Venezuela, ciki har da 'yan adawar dimokradiyya, kungiyoyin farar hula, tsoffin sojoji da 'yan jarida," in ji kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka Matthew Miller a cikin wata sanarwa.
Babban Lauyan Venezuela Tarek William Saab, ya sanar da cewa ana tuhumar mutanen da laifin yi wa gwamnatin Maduro zagon kasa, ko da yake bai ba da hujja ba. A cikin wata sanarwa mai tada hankali, ya gaya wa manema labarai cewa mutanen da aka tsare "sun amsa laifinsu tare da ba da bayanai game da shirye-shiryensu."
A cikin sabon rahotonta na kare hakkin dan adam da aka wallafa a cikin watan Maris na 2023, Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta lura cewa yayin da Venezuela ta kasance "jamhuriya mai bin kundin tsarin mulki kuma mai jami’yyu da yawa a hukumace, gwamnatin Nicolás Maduro na ikirarin iko da dukkan cibiyoyin al’uma." Daga cikin "manyan abubuwan cin zarafin bil'adama da gwamnatin ta aikata," Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ambaci manyan matsaloli game da 'yancin bangaren shari'a; gazawar ’yan kasa wajen sauya gwamnatinsu cikin lumana ta hanyar zabukan gaskiya da adalci, da kuma hana shiga harkokin siyasa ba tare da dalili ba.
Dangane da sabon umarnin kama mutane da tsare su, Miller ya lura cewa, "Kame ba tare da bin ka'ida ba ya saba wa yarjejeniyar shirin zabe da aka cimma a watan Oktoban 2023 tsakanin hadakar jam’iyyun adawa ta Unitary Platform da wakilan Nicolás Maduro. Amurka na kira da a kawo karshen cin zarafi na siyasa, ciki har da kai hare-hare kan ofisoshin yakin neman zaben 'yan adawa da duk wani yunkuri na dakile muradun dimokradiyyar al'ummar Venezuela ta hanyar tsoratarwa."
Miller ya ayyana cewa, “matakan da suka saba wa wasiƙar Yarjejeniyar Barbados za su fuskanci sakamako. Muna kira ga Maduro da wakilansa da su bi yarjejeniyar zaben, ciki har da bayyana takamaiman lokacin da za a yi zaben shugaban kasa na 2024 da kuma dawo da dukkan 'yan takarar siyasa neman takara."
"Amurka, na ci gaba da tallafa wa al'ummar Venezuelan a muradin su na ganin an maido da mulkin dimokradiyya cikin lumana." in ji Miller.
Dandalin Mu Tattauna