Wata kotu a Kenya ta tuhumi shugaban wata kungiyar asiri da ke azabtar da yara kanana da yunwa da kuma zalunci, lamarin da ya yi sandiyar mutuwar mabiyansa sama da 400.
Paul Nthenge Mackenzie da wasu mutane 38 da ake tuhuma sun ki amsa laifukan da ake tuhumar su da su, da suka hada da duka da kuma kashe yara ta hanyar yunwa da gangan, a cewar takardun kotun Mombasa da kamfanin dillancin labaran Faransa, AFP, ya gani.
Mackenzie, wanda tuni aka tuhume shi da laifin ta'addanci da kisa, ana zarginsa da ingiza mabiyansa su kashe kansu da yunwa domin su hadu da Yesu al-masihu.
A ranar 6 ga watan Fabrairu ne aka shirya wata kotu a birnin Malindi da ke gabar tekun kasar, za ta yanke hukunci idan har Fasto yana da koshin lafiya don fuskantar karin tuhumar kisan kai.
An kama shi a watan Afrilun 2023 bayan da aka gano gawarwakin mutane a dajin Shakahola da ke kusa da tekun Indiya.
Binciken gawarwakin mutane ya nuna cewa akasarin mutanen 429 , ciki har da yara, sun mutu ne saboda yunwa wasu kuma da alama an shake su ne.
Dandalin Mu Tattauna