A yayin ziyarar, sakataren zai yi tsokaci kan yadda Amurka ta kara inganta hadin gwiwar Amurka da Afirka tun bayan taron Shugabannin Amurka da Afirka, da suka hada da yanayi, abinci, da kiwon lafiya.
Mazauna birnin Ibadan, a jihar Oyo da ke kudu maso yammacin Najeriya, mai yawan jama'a sun ji karar fashewar wani abu mai karfi da misalin karfe 7:45 na dare, lamarin da ya haifar da firgici yayin da da dama suka tsere daga gidajensu.
Ana zargin wani likita a birnin Jos da sace kodar wasu marasa lafiya ba tare da saninsu ba. ‘Yan sanda sun kama likitan, kuma sun kulle asibitin na shi.
Waiwayar wasu daga cikin manyan al’amura da suka faru a wannan shekara mai karewa, ciki hadda rantsar da shugaba Bola Tinubu a matsayin shugaban kasar a Mayu, da kuma cire tallafin man fetur da ya kara tsananin rayuwa a tsakanin jama’a.
An dakatar da wani jirgin saman da zai nufi kasar Nicaragua dauke da fasinjoji sama da 300 daga kasar Indiya a Faransa bisa zargin “fataucin mutane” a cewar hukumomi a ranar Juma’a.
"An tabbatar da cewa an kashe Maalim Ayman ne a wani farmakin hadin gwiwa da sojojin kasar Somaliya tare da taimakon sojojin Amurka suka yi a ranar 17 ga watan Disamba," in ji Daud Aweis a shafinsa na X da yammacin ranar Alhamis.
A ranar Litinin da ta gabata ne Hukumar Kula da Hada-Hadar Kudi ta Amurka (SEC) ta gurfanar da dan kasuwan nan na Najeriya Dozy Mmobuosi da wasu kamfanoni uku wanda shi ne shugabansu, inda ake zargin su da damfarar masu zuba jari.
"Kotun koli ta Colorado ta fitar da wani hukunci mai cike da kura-kurai a daren yau kuma za mu shigar da kara cikin gaggawa zuwa kotun kolin Amurka." in ji mai magana da yawun yakin neman zaben Trump
Babbar Kotun Tarayya da ke birnin tarayya, Abuja ta haramta wa tsohuwar Ministar Mata da Walwalar Al’umma, Pauline Tallen sake rike wani mukamin gwamnati.
Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta ce ba ta gamsu cewa sojojin Najeriya za su gudanar da irin bincike na gaskiya ba a game da harin da sojoji suka kai a kauyen Tudun Biri a Kaduna, wanda ya halaka sama da fararen hula 100.
Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta bayyana muhimmancin lafiya da cikakken lafiyar jiki, na kwakwalwa da kuma mu’amala da mutane, kana hakan baya nufin rashin lalura gaba daya.
Tsohon Ma'aikacin Sashen Hausa Alhaji, Kabiru Usman Fagge ya rasu a nan Amurka sakamakon rashin lafiya.
Dokta Chukwuemeka Ezeife, wanda jigo ne a kungiyar kabilar Igbo ta Ohaneze Ndigbo, ya rasu ne a babban asibitin Tarayya da ke Abuja a sakamakon rashin lafiya.
Wasu ‘yan bindiga sun yi wa ayarin motocin kwanton bauna a kudancin Najeriya, inda suka kashe sojoji hudu da wasu farar hula biyu tare da yin garkuwa da wasu ma’aikatan kasar Koriya biyu, kamar yadda ‘yan sanda suka bayyana a yau Laraba.
Shahararren dan wasan Nigeriya, Victor Osimhen ya zama dan wasa daga nahiyar Afirka na farko da ya lashe kyautar gwarzon dan wasan da yafi kowa zura kwallo a raga a gasar Siriya A ta kasar Italy.
Wakokin Jemiriye sun samu karbuwa sosai ba a Legas kadai ba har ma da kasashen duniya.
Kwararriyar 'yar jarida kuma tsohuwar ma’aikaciyar gidan talabijin na NTA, Aisha Bello ta rasu ranar Lahadi sai dai ba a bayyana sanadin mutuwar ta ba.
Hira da Zaliha Lawal, Darektar shirin cibiyar Connected Development da aka fi sani da CODE a game da kasafin kudin 2024 da shugaban Najeriya Tinubu ya gabatar a majalisar tarayyar kasar a kwanan nan, inda ta tabo batun tattalin arziki da harkokin kiwon lafiya.
Binciken baya bayan nan sun nuna cewa, alkaluman mutanen da suke fama da matsalar kadaici da kuma nesanta kansu da mutane yana dada karuwa, kuma ya fara zama matsalar lafiyar al’umma.
Yayin da Isra’ila ke ci gaba da kai hare-hare da ya yi sanadiyar karuwar asarar rayukan fararen hula, Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya yi kira da a yi amfani da wani karfin ikon da ba kasafai ake amfani da shi ba a wannan makon.
Domin Kari