Najeriya wadda ita ce ke shugabar kungiyar ta ECOWAS, ta yi tsokaci a karon farko kan sanarwar da kasashen uku karkashin jagorancin mulkin soja suka fitar a ranar Lahadin da ta gabata cewa, nan sun fice daga kawancen yankin da aka kwashe kusan shekaru 50 ana yi, ba da wata-wata ba.
Ma'aikatar harkokin wajen Najeriya a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce wadanda ke neman ficewa daga kungiyar ECOWAS ba suna yi da kyakkawar manufa ba.
Ya zuwa yanzu dai kungiyar ECOWAS ba ta ce uffan ba kan matakin, wanda zai iya kara raunana kungiyar a kokarin da take yi na dakile yunkurin juyin mulkin demokradiyya a yankin yammacin Afirka.
Tun da farko dai ma'aikatun harkokin wajen Mali da Nijar sun sanar da hukumar ta ECOWAS matakin da suka dauka a rubutacciyar sanarwar da aka fitar ranar Litinin, da kamfanin dillancin labarai na Reuters ya gani.
Najeriya ta ce har yanzu tana so ta cigaba da hulda da kasashen uku.
Matakin ficewar nasu, wanda aka sanar a cikin wata sanarwar hadin gwiwa a lokaci guda a gidajen talabijin na kasar, wani rauni ne ga yunkurin hadewar kungiyar a yankin bayan ta dakatar da juyin mulkin uku da ya biyo baya.
Dandalin Mu Tattauna