Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ECOWAS Ta Mayar Da Martani Kan Ficewar Burkina Faso, Mali da Jamhuriyar Nijar Daga Cikinta


Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS)  ko CEDEAO
Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS)  ko CEDEAO

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ta ECOWAS ko CEDEAO ta mayar da martani kan sanarwar ficewar kasashen Burkina Faso, Mali da Jamhuriyar Nijar daga cikinta.

Kungiyar ta ECOWAS ta bayyana hakan ne a wata sanarwar da ta fitar, inda ta jaddada aniyarta ta aiki sau da kafa da Burkina Faso, Mali, da Jamhuriyar Nijar don maido da aiki da kundin tsarin mulki a kasashen.

Ko da yake kungiyar ta ce har yanzu ba ta samu wata wasika daga kasashen uku da ke nuni da aniyar janyewa daga cikinta ba, har yanzu tana kan bakanta na ganin cewa an sami masalaha ta hanyar tattaunawa da kasashen.

Kungiyar ECOWAS ta kuma jaddada muhimmancin kasashen na Burkina Faso, Nijar da Mali na ci gaba da zama a matsayin mambobinta.

Har yanzu dai sojojin da suka kifar da gwamnatocin farar hula ne ke jan ragamar wadannan kasashe da ke fama da matsalar tsaro a yankin Afrika ta yamma.

A ranar Lahadi ne kasashen Mali, Burkina Faso, da Nijar da ke karkashin mulkin soja suka bada sanarwar ficewa daga sahun kasashe mambobin ECOWAS sakamakon abin da suka kira rashin gamsuwa da yadda kungiyar ta kauce wa ainahin turbar da aka kafa ta, hasali ma su na zarginta da kasancewa barazana ga zaman lafiya.

Kakakin majalissar CNSP Kanal Abdourahamane Amadou ne ya bayar da sanarwar hadin gwiwar kasashen uku a kafar talabijin na RTN Mallakar gwamnatin Nijar da karfe 2 na ranar Lahadi 28 ga watan Janairun 2024, kwana daya kenan bayan ziyarar da wasu ministocin Burkina Faso da na Mali suka kai birnin Yamai.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG