Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mutum 7 Sun Mutu Sakamakon Zaftarewar Kasa A Philippines


Zaftarewar kasa a Philippines
Zaftarewar kasa a Philippines

Masu aikin ceto sun kwaso gawarwaki bakwai daga cikin laka, ciki har da na yara. Wasu mutane hudu kuma har yanzu ba a gansu ba, Rocris Idul ya shaida wa AFP.

Akalla mutane bakwai ne suka mutu sakamakon zaftarewar kasa da ta afkawa wani gida a kudancin kasar Philippines a ranar Alhamis, wani jami'in kula da bala'i ya ce, ana kuma kyautata zaton adadin wadanda suka mutun zai karu.

Lamarin ya faru ne da safe a yankin da ake hako zinari mai tsaunuka na lardin Davao de Oro da ke tsibirin Mindanao, inda ruwan sama kamar da bakin kwarya ya haddasa ambaliya da zabtarewar kasa a wannan mako.

Masu aikin ceto sun kwaso gawarwaki bakwai daga cikin laka, ciki har da na yara. Wasu mutane hudu kuma har yanzu ba a gansu ba, Rocris Idul ya shaida wa AFP.

An fitar da mutane uku da ransu, ciki har da daya wanda ya samu munanan raunuka, in ji Idul.

Magajin garin Monkayo, Manual Zamora, ya ba da gargadi a ranar Laraba ga mutanen da ke zaune a cikin "mummunar haɗari" na gundumar da har yanzu su basu bar gidajensu, shugaban ma'aikatansa, Rodielyn Manugas, ya shaida wa AFP.

An umarci makarantu a karamar hukumar da su dakatar da karatu a ranar Juma’a, inda ake sa ran za a samu ruwan sama mai karfi a yankin.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG