A ranar Litinin ne aka rantsar da Joseph Boakai a matsayin Shugaban Kasar Laberiya bayan nasarar da ya samu a zaben da ya yi a kan tsohon tauraron kwallon kafa, George Weah, yayin da zai fuskanci kalubalen magance talauci da cin hanci da rashawa.
Bikin nasarar da aka gudanar a majalisar ya samu halartar Shugaban Kasar Ghana Nana Akufo-Addo da jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Linda Thomas-Greenfield.
Boakai gogeggen dan siyasa ne kuma ya yi aiki a matsayin Mataimakin Shugaban Kasa daga 2006 zuwa 2018 a karkashin mace ta farko ta da zama Shugabar Kasar Laberiya, Ellen Johnson Sirleaf, kafin Weah ya doke ta da kyar a zaben 2017.
Zaɓen watan Nuwamba a ƙasar da ke yammacin Afirka ya kasance cikin lumana a yankin da ya fuskanci juyin mulkin da sojoji suka yi a shekarun baya a Mali, Burkina Faso, Guinea da Nijar.
Sai dai kasar da ke da mutane miliyan biyar tana fama da matsalar cin hanci da rashawa, da matsanancin talauci da rashin tsarin adalci, bayan shafe shekaru ana yakin basasa da barkewar cutar Ebola.
Dandalin Mu Tattauna