A yau Jumma'a ne Ministan yada labaran Pakistan ya ce manyan shugabannin fararen hula da na sojan kasar za su gudanar da wani taron nazari kan harkokin tsaro a kan takaddamar da ke tsakaninsu da Iran, bayan da kasashen masu makwabtaka da juna suka kai hari da makami mai linzami kan sansanonin 'yan ta'adda a yankunan juna.
Firaministan rikon kwarya Anwaar-ul-Haq Kakar ne zai jagoranci taron kwamitin tsaro na kasa, kuma dukkanin hafsoshin sojojin kasar zasu halarci taron, kamar yadda minista, Murtaza Solangi, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters ta wayar tarho.
Solangi ya ce manufar taron ita ce yin nazari mai zurfi kan harkokin tsaron kasa bayan abubuwan da suka faru a Iran da Pakistan.
Hare-haren ramuwar gayya da kasashen biyu ke yi shi ne kutse mafi girma da aka gani a kan iyakokinsu a shekarun baya-bayan nan, lamarin da ya haifar da fargaba game da karuwar rashin zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya tun bayan barkewar yakin Isra'ila da Hamas a ranar 7 ga watan Oktoba.
A gefe guda kuma, ita ma Iran ta fada a yau Juma'a cewa ta yi nasarar gudanar da atisayen tsaro ta sama ta hanyar amfani da jirage mara matuka da aka kera domin dakile hare-haren wuce gona da iri a yankin da ya tashi daga kudu maso yammacinta zuwa gabar tekun kudu maso gabashin kasar, a daidai lokacin da ake kara samun tashin hankali a yankin.
A ranar Alhamis Pakistan ta kaddamar da hare-hare ta sama kan wasu da ta ce 'yan aware ne a cikin Iran a wani harin ramuwar gayya kwanaki biyu bayan da Tehran ta ce ta kai hari kan sansanonin wata kungiya a yankin Pakistan.
Atisayen na kwanaki biyu da aka fara a ranar Alhamis, ya shafi wani yanki daga Abadan, da ke kudu maso yammacin lardin Khuzestan, zuwa Chahbahar da ke kudu maso gabashin Sistan da lardin Baluchistan mai iyaka da Pakistan da Afghanistan.
Dandalin Mu Tattauna