Adadin wadanda suka mutu sakamakon harin tankokin yaki a sansanin Majalisar Dinkin Duniya a babban birnin Khan Yunis da ke kudancin Gaza ya karu zuwa 12, kamar yadda Thomas White, wani babban jami'in agaji na Majalisar Dinkin Duniya ya sanar a yau Alhamis.
"A yanzu an tabbatar da mutuwar mutane 12 tare da jikkata sama da 75. 15 daga cikinsu suna cikin mawuyacin hali," in ji Thomas White, Daraktan Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Gaza ta UNRWA.
A ranar Laraba, wasu tankokin yaki guda biyu sun kai hari a matsugunin Majalisar Dinkin Duniya a Khan Yunis inda dubban Falasdinawa da suka rasa matsugunansu suka fake, in ji shi.
Shugaban hukumar ta UNRWA Philippe Lazzarini ya ce harin bama-baman “rashin kula da muhimman ka’idojin yaki ne”.
An sanya wani babban alama da ya nuna alamun cibiyar Majalisar Dinkin Duniya ce a fili kuma an sanar da hukumomin Isra'ila, in ji shi a shafin X, wanda a da ake ka fi sani da Twitter.
Da aka tambaye Isra’ila game da harin tankar, rundunar sojin Isra'ila ta ce "ana ci gaba da yin nazari sosai kan ayyukan sojojin da ke kusa da wajen", inda ta kara da cewa, tana tsammanin aikin Hamas ne".
Sojojin Isra'ila ne kadai aka sani da ke da tankokin yaki a zirin Gaza.
Ita ma Amurka ta yi Allah wadai da harin bam din, Kakakin Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka, Vedant Patel ya ce "dole ne a kare fararen hula kuma a mutunta yanayin kariya na cibiyoyin MDD".
Dandalin Mu Tattauna