A bayan da ya koma Iran shekaranjiya lahadi domin tuntubar hukumomi, Zarif ya koma Vienna tare da shugaban shirin nikiliyar Iran Ali Akbar Salehi, wanda ya ke jinyar wata rashin lafiya.
Bayan da suka dawo Zarif ya gana da sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry.
Mr Kerry dai ya fito daga taron yana fadin cewa “mun yi kyakkyawar tattaunawa”
Kafofin yada labarai mallakar gwamnatin Iran sun ambaci Zarif yana fadin cewa sake komawar Salehi wajen zaman, duk da rashin lafiyar da yake fama da ita, ya nuna cewa lallai Iran ta dauki shawarwarin da ake yi da muhimmanci. Ya kuma kara da cewa abinda ake bukata shine “kuduri a siyasance” daga manyan kasashen duniya da ke kan teburin tattaunawar don bangarorin biyu su iya cimma karbabbiyar, dorarriyar shawara.
Yau Talata ce ranar cikar wa’adin yarjejeniyar. Iran da manyan kasashen duniya daga kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya guda 5 tare da kasar Jamus, suna kokarin cimma yarjejeniya da zai takaita damar da Iran ke da ita ta kera makamin nukiliya, yayin da su kuma zasu sassauto da takunkumin da aka kafa mata.