Shugaban kasar Amurka Barack Obama zai karbi bakuncin Firai Ministan Israila Benjamin Netanyahu a yau Laraba domin su yi tattaunawar da ake kyautata cewa za ta fi bada karfi kan batun nukiliyar Iran.
Za su gana a Fadar White House ne bayan jawabin da da Mr. Netanyahu yayi kwanakin baya a a zauren babban taron MDD in da ya furta cewa Iran kokari take yi ta yaudari kasashen duniya su dage ma ta takunkuman karya tattalin arziki, a lokaci guda kuma su bar ta ta kera makaman nukiliya.
Netanyahu yayi kashedin cewa idan Iran ta mallaki nukiliya hataarin ta zai fi na kungiyar Daular Islama mai gudanar da ayyukan ta a Iraki da Syria.
Gwamnatin kasar Iran dai ta dade a kan bakan ta na cewa shirin ta na nukiliya na zaman lafiya ne, kuma ta ce jawabin na Mr. Netanyahu wani abu ba ne illa ci gaban wata manufar yin zagon kasa da hana tattaunawar da ake yi da manyan kasashen duniya kan shirin ta na nukiliya.
Iran na so a dage ma ta takunkuman da suka yiwa tattalin arzikin ta illa, amma wani gungun kasashen da suka hada da Amurka da Birtaniya da China da Faransa da Rasha da Jamus na bukatar samun tabbaci daga gwamnatin kasar Iran cewa ba makaman nukiliya take son kerawa ba.