Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Houthi Sun Amince Da Shirin Tsagaita Wuta


Wasu dakarun kasar Yamal da suka koma marawa 'yan tawaye baya
Wasu dakarun kasar Yamal da suka koma marawa 'yan tawaye baya

Mayakan Houthi a kasar Yamal, sun ce sun amince da shirin tsagaita wuta na jin-kai da aka cimma na tsawon kwanaki biyar, wanda kasar Saudiyya ta yi tayi, wanda kuma zai fara aiki a ranar Talata mai zuwa.

Wannan sanarwa da mayakan suka fitar, na zuwa ne sa’oi kadan bayan da jiragen yakin dakarun da Saudiyyan ke jagoranta suka kai wani samame kan gidan tsohon shugaban kasar, Ali Abdullah Saleh, da ke Sana’a, babban birnin kasar.

Babu dai rahotanni da ke cewa Mr Saleh ya na gida a lokacin samamen.

A makon da ya gabata, Amurka da Saudiyya suka bayyana shirin tsagaita wuta na tsawon kwanaki biyar a Yamal, inda dakarun da Saudiyan ke jagoranta suke kai hare-hare akan ‘yan tawayen Houthi da ke kokarin mamaye manyan garuruwan kasar.

Ya zuwa yanzu wannan yaki ya, ya saka dubban mutane cikin halin kakanikayi.

A baya, sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry, ya tattauna da masu fada a ji a bangaren ‘yan Houthi, inda ya yi kira ga ‘yan tawayen da su amince da shirin tsagaita wutar.

Ana tunanin ‘yan tawayen wadanda mabiya akidar Shi’a ne, kuma suke goyon bayan Mr Saleh, suna samun taimako ne daga kasar Iran.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG