Firayim Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu yace Amurka da Isra'ila sun amince kan bukatar hana Iran mallakar makaman Nukiliya, amma sun sami sabani kan hanyar da za'a cimma burin.
Jiya Litinin Firayim Ministan ya furta wadannan kalamai, kwana daya kamin jawabinda zai gabatar a gaban majalisar dokokin Amurka. Gayyatar da aka yiwa Firayim Ministan ya gabatar da wannan jawabi ta janyo cacar baki a Amurka, domin an mika goron gayyatar ba tareda al'adar da aka saba ba ta tuntubar Fadar White House ta shugaban Amurka, wanda ya kara bayyana tsamin dangantaka tsakanin Mr. Netanyahu da shugaba Barack Obama.
Mr. Netanyahu yace rashin fahimtar da suka samu da Amurka ya samo asali ne domin Washongton ta fi damuwa ne da batun tsaro, ita kuma Isra'ila ta damu ne gameda batun rayuwarta baki daya.
Shugaban na Amurka ya amince da haka. A hira da yayi da kamfanin dillancin labarai na Reuters jiya Litinin, Mr. Obama yace akwai banbanci kwarai tsakanin gwamnatinsa da ta Isra'ila kan hanyoyin da zasu kai ga cimma buri da duka suke dashi na hana Iran mallakar makaman nukiliya.
Mr. Obama yaci gaba da cewa "idan har da gaske Iran ta amince zata tsaida shirin nukiliyarta na shekaru masu yawa kamar 10 inda yake ahalin yanzu, kuma zata maida hanun agogo baya kan ayyuka da ta cimma ahalin yanzu, idan muka sami haka, kuma muka sami tabbacin yadda zamu tantance tana mutunta hakan, babu wata hanya da zamu bi data fi haka wajen tabbatar mana cewa Iran bata kera makaman Nukiliya ba", inji Mr. Obama.
Duk da haka yace sabanin ba zai yi rauni ga dangantakar da take akwai tsakanin Amurka da Isra'ila ba.
Tunda farko a jiya litinin din, sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry yace, duk wata yarjejeniyar da Amurka zata amince da ita kan shirin Iran hakan zai tabbatar da lafiyar hukumomin kasa da ksa, musamman ma Isra'ila.