Wani jami’in rundunar sojin Amurka yace jiragen ruwan dakon kayan kasar Iran da ake zaton suna kan hanyarsu ta zuwa kaiwa ‘yan tawayen Houthi makamai ne a Yemen da yaki ya daidaita sun fara ja da baya suna nisantar kasar.
Jami’in da ya nemi a sakaye sunansa ya bayyana lamarin a matsayin alamar ci gaba mai kyau.
Sai dai yace ma’aikatar tsaron Amurka zata ci gaba da sa ido kan jiragen sosai.
Fadar White House tace ta ga shaidun da suka nuna cewa Iran ta samarwa ‘Yan Shi’a kungiyar Houthi a Yemen makamai. Ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta tura jiragen ruwan yakin Amurka zuwa tekun Yemen domin ganin cewa ba a toshe hanyar sufurin mashigin ruwan ba.
Jami’an soji sun musanta cewa, an tura jiragen ruwan ne da nufin kange jiragen ruwan Iran.
A Yemen, jiragen saman yakin dakarun hadin guiwa karkashi jagorancin kasar Saudi Arabiya sun kai hari kan wani yankin ‘yan tawaye jiya Alhamis kusa da tashar sufurin ruwa dake kudancin Aden.
A cikin makon nan kasar Saudi Arabiya ta sanar da cewa zata kawo karshen hare haren sama da take jagoranta amma zata koma ta ci gaba da kai hare hare idan ta kama tayi hakan.