Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka da Iran Sun Samu Dan Cigaba Akan Shirin Nukiliyar Iran


Tattaunawar Kerry da Zarif akan nukiliya
Tattaunawar Kerry da Zarif akan nukiliya

A karon farko Amurka da Iran sun bayyana samun cigaba akan shirin nukiliyar Iran.

Amurka da Iran jiya Litinin, suka bada labarin cewa sun "sami ci gaba" a shawarwarin da suke gudanarwa dangane da shirin nukiliyar, duk da haka sun ce da sauran aiki jawur a gabansu.

Duka sassan biyu sun ce tattaunawar da ake yi a birnin Geneva tsakanin sakataren harkokin wajen Amurka John kerry, da kuma takwaran aikinsa na Iran Mohammed Javad Zarif, da cewa "masu ma'ana ne da aka mai da hankali sosai". Sai dai Ministan harkokin wajen Iran Mr. Zarif ya gayawa kamfanin dillancin labaran Iran da ake kira Fars cewa "da sauran tafiya mai tsawo kamin a kai ga cimma yarjejeniya".

Wani babban jami'i a ma'aikatar harkokin wajen Amurka yace sassan biyu sun fito da batutuwa da suke hana cimma matsaya a fili, "abunda ba'a sani ba shine ko hakan zai kai ga kulla yarjejeniya". Sassan biyu suna kokari ne su cimma yarjejeniya kamin karewar wa'adi da suka gindayawa kansu watau 31 ga watan Maris su fidda tsari na cimma yarjejeniya, da zai taimakawa shawarwari na cimma wa'adi na dun dun dun, a ranar 1 ga watan Juli. A karkashin yarjejeniyar za'a tabbatar da cewa shirin Nukiliyar Iran na farar hula ne, idan an sami haka kasashen yammacin duniya zasu janye takunkumin karya tattalin arzikin da suka kakabawa Iran da suka durkusar da tattalin arzikin Farisa.

Ana sa ran za a ci gaba da shawarwarin ranar Litinin mai zuwa a Switzerland.

Amurka da wasu manyan kasashen duniya biyar suna kokarin ganin sun kawo karshen hanyoyin d a Farisa zata iya bi ta habaka makaman Nukiliya, yayinda Iran ta dage cewa shirinta na farar hula ne.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG