Shugaban Kasar Iran Hassan Rouhani ya na ci gaba da yin alkawarin cewa Iran za ta dade ta na tallafawa kasar Iraki a yakin da take yi da mayakan Daular Islama.
A yayin ziyarar da Firai Ministan Iraki Haider al-Abadi ya kai kasar Iran, Mr. Rouhani ya shaida ma sa cewa gwamnatin sa za ta marawa gwamnatin Iraki baya daga farko har karshe, kamar yadda Kamfanin dillancin labaran gwamnatin kasar Iran din ya fada a yau Talata.
Shugaban na kasar Iran ya ce kasashen yankin na bukatar hada karfi da karfe su yi keke da keke da ta'addanci. Ya ce Iran za ta ci gaba da baiwa Iraki makamai da kuma sojojin da za su bata shawarwari.
Mr. Abadi ya ce ta'addanci barazana ce ga duka kasashen yankin, kuma ya ce sun tabbata Iran za ta tsaya kafada da kafada tare da su. Ya ce ya zabi fara ziyarar sa ta farko zuwa wata kasar waje da Iran ne saboda kakkarfar huldar da ta zurfafa tsakanin kasashen biyu.