Shugaban Amurka Barack Obama yace wakilan Amurka dana Iran sun warware banbance banbance dake tsakaninsu kan shirin Nukiliyar Iran din, duk da haka yace a shirye yake Amurka ta janye daga shawarwarin idan har basu cimma daidaiton da Amurka ta gamsu dashi ba.
Shugaban na Amurka yayi magana ne cikin wani shirin tashar talabijin na CBS da aka nuna jiya Lahadi. Yace duk wata yarjejeniyar da aka kulla, tilas ta baiwa sifetocin kasashen yammacin duniya damar su tantancecewa Iran bata kera makaman Nukiliya.
Daga bisani a cikin wannan shirin mai suna "Face the Nation", Firayim Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu yace shi da shugaba Obama "suna da buri daya" na hana Iran mallakar makaman Nukiliya, inda suka sami sabani shine hanyar da za'a bi a sami biyan bukata.
Iran dai ta dage cewa shirin Nukiliyarta na farin kaya ne. Amma Firayim Ministan Isra'ila yace shi bai yarda da tantancewar gwamnatocin 'yan malaka'u ba.