Shugaban addinin yayi wannan furuci ne a yayinda mashawarta daga kasar sa da kuma giggan kasashen duniya suka yi kusan cimma yarjejeniya akan shirin nukiliyan Iran.
Bangarorin suna aiki ne akan dala dalan shirin rage ko kuma dakatar da shirin nukiliyan Iran na tsawon shekaru goma, ita kuma a saka mata ta hanyar sassauta takunkunmin dake raunana tattalin arzikin kasar.
A watan Afrilu bangarorin suka tsayar da ranar talatin ga wannan wata na Yuni a zaman wa'adin da suka gitta wa kansu na cimma jadawalin yarjejeniyar.
Ayatollah Khamenei yace kasar sa ba zata yarda ta dakatar da shirin nukiliyan ta na tsawon shekaru goma ko shekaru goma sha biyu ba.. Haka kuma ya jaddada cewa Iran ba zata bari spectocin bincike zuwa ko kuwa kai ziyara masana'antun sojan ta a zaman wani bangare na tabbatar cewa Iran tana mutunta ka'idodin yarjejeniyar ba.
Bugu da kari kuma yace kasar sa tana son a dage takunkunmin da aka aza mata da zarar an kula yarjejeniya.