Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Zata Kare Kawayenta Na Yankin Gulf


Shugaba Obama da Yariman Bahrain
Shugaba Obama da Yariman Bahrain

Yayin da suke taron koli na yakin gulf shugaban Amurka ya fito fili yace Amurka zata kare kawayenta har karfin soji.

Shugaba Brack Obama yace Amurka ta kuduri anniyar tabbatar da tsaron kawayenta na kasashen da suke yankin Gulf, kuma zata yi amfani da karfin soja idan suka fuskanci wata barazana.

Mr. Obama ya jagoranci taron koli na shugabannin kasashe da manyan ministoci na kungiyar kasashen da suke yankin Gulf su shida a gandun shakatawa na shugaban Amurka da ake kira Camp David dake arewa da nan birnin Washington, a jiya Alhamis. Cikin wadanda suka halarci taron har da yerima mai jiran gado na kasar Saudiyya da na'ibinsa, sarakunan Kuwait da Qatar, da manyan jami'an gwamnati daga kasashen Bahrain, da Oman, da kuma hadaddiyar daular larabawa.

Bayan taron, shugaban na Amurka yace ya "fito fili" lokacin taron cewa Amurka zata kare kawayen nata daga yankin Gulf, daga duk wata barazana daga wata kasar waje, kuma Amurka da kasashen "zasu yi amfani da duk wata hanya ciki harda karfin soja".

"Shugaban yace "yankin yana ganin sauye sauye iri-iri, da kuma manyan kalubale".

Shugabannin kasashen da suke yankin Gulf , sun halarci taron kolin ne da nufin samun tabbaci daga shugaban na Amurka cewa hukumomin da suke Washington sun kuduri anniyar tabbatar da tsaronsu.

Mr. Obama yace Amurka zata kara kokarin ganin cewa kasashen sun kimtsawa tunkarar duk wata irin barazana. Matakan zasu hada da kara atisayin soja, da girka garkuwa daga makamai masu linzami, da kuma zama cikin shirin ko-ta-kwana.

Kasashen da suke yankin na Gulf suna nuna damuwa cewa muddin aka cimma yarjejeniya tsakanin babbar abokiyar hamayyarsu Iran da manyan kasashen duniya, zai kai ga matakin janye takunkumin karya tattalin arzikinDA aka kakabawa Iran, matakin zai baiwa Iran damar zama kasa mai karfi da tasiri a yankin.

Mr. Obama yace yana farin cikin ganin yanzu shugabannin kasashen yankin suna bada cikakken goyon bayansu ga yarjejeniyar d a zata hana Iran kera makaman nukiliya, tareda sanin cewa hakan zai taimaka musu.

Duk da haka Mr. Obama yace sai ta yiwu Iran zata cigaba d matakan tada zaune tsaye a yankin bayan da aka cimma yarjejeniya kan shirin Nukiliyar ranar 30 ga watan Yuni.

Ministan harkokin wajen kasar Saudi Arabiya Adel al-Jubeir yace "ba'a taba yin taron kolin irinsa ba", ya ce taron yayi tasiri ainun.

XS
SM
MD
LG