Majalisar dattijan Amurka ta amince da wani kuduri da zai baiwa majalisun dokoki ikon nazarin da kuma kin amincewa da duk wata yarjejeniyar kasa da kasa da Amurka ta kulla da nufin dakatar da shirin Nukiliyar Iran.
Wakilan majalisar dattijan su 98 ne suka amince da kudurin wakili daya yaki.Yanzu dokar zata tafi majalisar wakilai inda ake sa ran majalisar zata yi muhawara akanta makon gobe.
Shugaba Barack Obama da farko ya nuna adawa da dokar wacce zata tantance yarjejeniyar da Amurka da wasu manyan kasashen duniya biyar suke shawarwari da hukumomin Farisa da nufin takaita karfin kasar na kera makaman nukiliya. Duk da haka yace zai saka hanu kan dokar idan majalisun dokokin suka amince da ita.
Dokar zata baiwa majalisun kwanaki 30 su duba yarjejniyar da sharadin kin amincewa da ita.
Ahalin yanzu dai Iran tana mataki na karshe a shawarwari da take gudanarwa da kasashe biyar masu kujeru na din din din a akwamtin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da kuma Jamus da zummar takawa shirin nukiliyarta birki. Idan ta amince da yarjejeniyar, za’a janye takunkumin karya tattalin arziki da kasa da kasa da Amurka da kuma tarayyar turai suka kakaba mata. Amma a cikin kwanaki 30 da majalisar dokokin Amurka zata yi nazarin yarjejeniyar shugaba Obama ba zai iya janye takunkumi da Amurka ta azawa Iran ba.