Sakataren harkokin wajen Amurka John kerry da takwaran aikinsa na Iran Mr. Javad Zarif, sun kuma sake ganawa jiya Litinin a Switzerland, a ci gaba da yunkurin da suke yi na samun matsaya nan da karshen watan nan, a shawarwari da suka dauki lokaci mai tsawo ana yi kan shirin Nukilkiyar Iran.
Shawarwarin sun hada da sakataren hukumar makamshi ta Amurka Ernest Moniz, da kuma shugaban hukumar nukiliya na Iran Ali Akbar Salehi. Wadannan jami'an biyu sun gana ranar Lahadi domin shawarwari ta fuskar fasaha gameda shirin Nukiliyar Iran.
Bayan ganawa da Kerry na tsawon sa'o'i hudu, tawagar jami'an Iran din sun tafi Brussells domin ganawa da ministoci daga tarayyar turai.
Manyan kasashen duniya shida suna kokari su cimma jadawalin yarjejeniya da Iran kamin karshen wata da nufin tsaida shirin Nukiliyar Iran din mai zurfi na akalla shekaru 10, idan aka sami haka sannu a hankali a janye takunkumin karya tattalin arziki da aka kakakawa Farisar.