An dawo da tattaunawar da ake kan batun nukiliya tsakanin kasar Iran da manyan kasashe shida na duniya jiya Laraba a birnin Vienna, ana tattaunawa ne kan wasu batu masu sarkakkiya kan sasantawar da ake kokarin yi.
An dai tsaida 30 ga watan Yuni a matsayin wa’adin wannan tattaunawa da ake yi, don hana kasar Iran kera makaman Nukiliya, yayin da ake kara rage karfin takunkumin dake kan kasar .
Kasar Amurka dai tace ta na da shaidar cewa kasar Iran ta bai wa ‘yan tawayen Houthi na Yemen makamai. Kuma ta aika da jirgin ruwan yaki zuwa can kusa da kasar Yemen ‘din.
Jami’an Amurka sun ce zasu cigaba da matsawa kasar Iran ‘din lamba kan batun Amurkawan dake tsare da kuma Amurkawan da suka ‘bace a Iran ‘din, amma sun ce wannan magana daban ta ke da tattaunawar da akeyi ta nukiliya.