Dr. Umar Duhu, na cikin ‘yan takara a yankin Madagali daya daga cikin yankunan da ake kokarin kwatowa, yace sunyi mamaki da matakin dage zabe da aka dauka.
“Kuma ina so in fada da kakkarfar murya cewa maganar dage zabennan, sunyi don kansu ne, ba domin mu mutanen da ‘yan ta’adda suka kore mu daga gidajenmu ba,” a cewar Dr. Duhu.
Shima Alhaji Abdulrahman Kwacam dake yankin Mubi, wanda ba’a dade da kwato yankin ba daga hannun mayakan Boko Haram yayi bayanin cewa “shugaban sojoji na ruwa na Najeriya, ya tabbatar da cewa yana da tsaro, wanda ya gayawa duniya za’a kai kayan zabe duk inda ake so. Shugaban ‘yan Sandan Najeriya shima yace a shirye jami’ansa suke su gudanar da wannan zabe. Sannan zaben baki dayanta, awa 24 ne za’a yi a gama, a ce babu tsaro da za’a tsare wannan zabe, wannan maganar banza ce”.
Kamar sauran kungiyoyi, suma mata ba’a barsu a baya ba wajen tofa albarkacin bakinsu.
“Bamu firgita ba, ko shekara mai zuwa ne, muna jira zamuyi zabe, talakawa suna tare da mu” a cewar Hajiya Hauwa Ibrahim Bato a Jihar Adamawa.
Kawo yanzu dai jama’a na cigaba da gudanar da harkokinsu cikin lumana.