Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015: Amurka Tayi Bakin Cikin Dage Zaben Najeriya


Ziyarar John Kerry a Najeriya.
Ziyarar John Kerry a Najeriya.

Sakatare Kerry, yace kada Najeriya ta fake da batun tsaro ta yiwa demokuradiyya karan tsaye.

Amurka ta bayyana bakin cikin samun labarin cewa an dage zaben Najeriya

A cikin sanarwa da sakataren harkoin wajen Amurka John kerry ya bayar, ya bayyan bakin cikinsa kan dage zaben da aka shirya da za'a fara ranar Asabar 14 ga watan nan.

Mr. Kerry yace Amurka ba zata lamunta ba wajen yiwa hukumar zabe shishshigi, kuma yana da muhimmanci kada gwamnatin Najeriya ta fake da dalilan tsaro wajen yiwa tsarin Demokuradiyya karan tsaye.

Yace hukumomin kasa da kasa suna sai do sosai yayinda hukumomin Najeriya suke shirya wa zabe a sabon lokacin da aka bayar. Mr. Kerry yace, Amurka tana jaddada muhimmancin ganin ba'a sake fuskantar wani tsaiko wajen gudanar da wannan zabe ba.

Sakataren harkokin wajen na Amurka yace "kamar yadda na karfafa lokacinda na ziyarci Legas, muna goyon baya ganin an gudanar da zabe sahihi cikin walwala bisa tsarin zabe mai inganci, muna kuma sabunta kira da muka yiwa dukkan 'yan takara da magoya bayansu, da dokacin al'umar Najeriya su kai zuciya nesa, su kaucewa duk wani lamari da zai janyo tarzomar siyasa".

XS
SM
MD
LG