Janaral Buhari yace ya zama wajibi sabuwar ranar zaben ta zama tamkar zanen dutse domin jam'iyyarsa ba zata cigaba da yadda da shishshigi a lamarin hukumar zabe ba.
Janaral Buhari yace abun da suka sa a gabansu shi ne zaman lafiya da wadatar al'umma. Kuma tunda abun da INEC tayi yana cikin kai'dojin mulkin Najeriya babu abun da zasu yi saidai su yi hakuri ranar zaben ta zo. Amma a cikin kundun tsarin mulkin Najeriya wanna ita ce dabara ta karshe da zasu yi. Ba zasu iya canza ranar zaben ba kuma. Amma su zasu jajirce a yi zaben ranar 28 ga watan Maris.
Bayan ranar zaben idan bata bari anyi zaben ba to ko gwamnati ta mikawa sojoji mulki ko tace ta kwace mulki babu ruwanta da dimokradiya. Sauran kuma ya rage ga 'yan Najeriya. Su ne suka san yadda zasu yi dasu.
To saidai sakataren kwamitin amintattu na jam'iyyar PDP Sanata Walid Jibrin ya musanta makarkashiyar dage zaben. PDP ba ita ce ta sa a canza ranar zabe ba. Saboda tana mulki ba za'a dora mata alhakin abun da ya faru ba. PDP wai bata da niyyar kara kwana daya akan wa'adin mulkinta. Jam'iyyun hamayya yakamata su kwantar da hankalin magoya bayansu. Kada su tada hankali. Su tsaya su ga yadda lamarin zai kare.