Jama'a na cigaba da bayyana ra'ayoyinsu domin dage zabuka da hukumar zabe tayi, wato INEC, har sai zuwa wani lokaci nan gaba.
A yayin da wasu ke ganin dage zaben yayi daidai wasu kuma gani suke hukumar zaben bata kyauta ba. A cewar wasu idan da hukumomin Najeriya da gaske suke da sun dauki mataki akan ta'adancin Boko Haram tuntuni cikin shakaru biyar din da suka wace. Ba yanzu ba ne zasu tashi da sunan yakar Boko Haram gadan-gadan.
Baraden Lafiya Alhaji Musa Liman Kwande yace dage zaben na kan ka'ida. Tunda jam'an tsaro sun ce hankalinsu na kan jihohin dake fama da ta'adancin Boko Haram ba zasu iya tabbatar da tsaro ba lokacin zabuka to dole ne a dage zabukan.
Musa Goji kuma cewa yayi jama'a su yi hakuri su bar komi ga Allah. Yace komi nufin Allah ne. A yi hakuri a bar komi ya zama nufin Allah.