Yau Asabar ake sa ran shugaban hukumar zabe a Najeriya Parfessa Attahiru Jega, zai gana da wakilan jam'iyun siyasar Najeriya, inda ake sa ran hukumar zata fito fili ta tabbatar da lokacin da za'a gudanar da wannan zaben, ko akasin haka.
Wannan zaman na yau Asabar, ya biyo bayan shawarwari na fiyeda sa'o'i biyar da Majalisar kasa karkashin jagorancin shugaba Goodluck Jonathan, ta gudanar musamman kan harkar zaben nan ranar Alhamis.
Kamin taron dai, rade-rade, tareda zargi daga sassan daban daban, ,musamman daga babbar jam'iyyar hamayya ta APC, cewa, gwamnati tana kokarin amfani da taron majalisar ta kasa domin ta dage zaben.
Majalisar wacce ta kunshi tsoffin shugabannin kasa, da manyan alkalai, da manyan jami'an tsaro, tareda shugaban hukumar zabe ta INEC, Parfessa Attahiru Jega, duk sun halarci taron.
In banda tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo, dukkan tsoffin shugabannin Najeriya, ciki harda Janar Muhammadu Buhari, duk sun halarci taron.