Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015: Kiraye-kirayen Kungiyoyi Game da Zabe


Yayinda ake ta shirye-shiryen zaben ranar 14 ga watan nan, kungiyoyi da sauran al’umma na cigaba da fadakarwa akan abinda ya kamata ‘yan Najeriya su kula da shi dangane da zabe. Kungiyoyin sun hada da muryar talaka, Rai dangin goro da ma’abota masu sauraron kafafen yada labarai.

Yayinda ake ta shirye-shiryen zaben ranar 14 ga watan nan, kungiyoyi da sauran al’umma na cigaba da fadakarwa akan abinda ya kamata ‘yan Najeriya su kula da shi dangane da zabe. Kungiyoyin sun hada da Muryar talaka, Rai dangin goro da ma ma’abota masu sauraron kafafen yada labarai.

Malam Baba Iyali Kawu, ya ce ya kamata a duba abinda dan takara yayi kafin ace za a zabe shi ba dai kawai don ya ce a zabe shi ba, kuma me zai yi. Malam Kawu kuma yayi kira ga matasa da su guji bada damar yin amfani da su wajen bangar siyasa.

Shi kuma Malam Yusuf Osama na kungiyar muryar talaka cewa yayi, karfin yin zabe na ga katin zabe, amma kuma bayan duk kiran da malaman addini keyi na aje a karbi katunan wasu da yawa basu karba ba.

Malam Inusa Adamu Mohammed na kungiyar Rai dangin goro, yayi kira ga hukumar zabe da ta yi wani abinda duniya zata yaba mata, ta fidda sakamakon zabe na gaskiya.

Wani kusa a jam’iyyar PDP ta jihar Adamawa yayi kira ga ‘yan siyasa da su kiyaye abinda zai kawo tashin hankali ya kuma ce zage-zage ba zai haifar da alkhairi ba amma kada kuri’a ga wanda ya dace.

Masani a harkar shari’a Mr. Sunday Joshua, ya ce a yanzu haka dai kowa ya daura damarar zabe. Ya kuma kara da cewa harkar tsawon Najeriya har yanzu abun ya ki ci ya ki cinyewa duk da gwamnati na daukar matakai, don haka ya zama dole a yi zabe kamar yadda aka shirya duk da tirjiyar da wasu keyi.

Kiraye-kirayen Kungiyoyi Game da Zabe - 3'40"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00

XS
SM
MD
LG