Ahmadu Ketu Namala, Malamin kimiyya a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Modibbo-Adama dake birnin Yola.
“Ni a matsayi na, na wanda yayi siyasa a baya, kuma wanda yake kaunar zaman lafiya, ni abunda zan fada, duk shure-shuren da akeyi, ana neman wata wuta ta tashi ne, amma mutanen Najeriya, muyi hakuri, mu jure, mu daure, mu sani, komai daga wannan abun, baza a daga shi ya fita daga cikin tsarin da aka yi ba, a dokokin zabe.”
Dr. Namala ya kara da cewa “to koda an daga ne, ayi hakuri”.
“Yanzu maganar bada tsaro a arewa maso gabas, kullum kowani mako, sai ace mutanen Najeriya suyi hakuri, yanzu-yanzu za’a kori Boko Haram, kullum sai an fito, sati daya, wata daya, har mun shiga shekaru nawa yanzu?
Hukumar Zabe mai Zaman Kanta a Najeriya, INEC ta dage ranakun babban zaben dake tafe na shekarar 2015 da aka shirya wakana ranakun 14 da 28 na watannan na Fabrairu, saboda hukumomin tsaro dake karkashin shugaban kasa sunce baza su samar da tsaro ba.
A lokacin da yake bayyana lamarin ne a gaban manema labarai a birnin Tarayya Abuja Asabar dinnan, shugaban Hukumar, Attahiru Jega yace za’a gudanar da zaben shugaban kasa da ‘yan majalisu ran 28 ga watan Maris, sannan a gudanar dana gwamna da ‘yan majalisar jihohi ranar 11 ga watan Afrilu.
Mr. Jega yace an dage ranar zaben ne, saboda jami’an tsaro sun bayyana cewa baza su bada kariya ba ranakun 14 da 28 na watan Fabrairu.
Shugaban INEC yace jami’an tsaron sun gayawa hukumarshi cewa zasu fara yaki na musamman na makonni shida akan Boko Haram ne a arewa maso gabashin Najeriya, saboda haka ‘yan Najeriya basu bukatar harkokin zabe ya dauke musu hankali.