Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015: Najeriya Ta Dage Zabe Zuwa Watan Maris


'Yansanda suke bada kariya a Abuja ga masu zanga zanga kan dage zabe ranar Asabar.
'Yansanda suke bada kariya a Abuja ga masu zanga zanga kan dage zabe ranar Asabar.

An bada dalilan tsaro a zaman daya daga cikin dalilai da suka janyo tsaikon.

Asabar dinnan ne Najeriya ta bada sanarwar ta dage zaben da aka shirya za'a fara ranar 14 ga wannan wata. An dage zaben ne na tsawon mako shida saboda dalilan tsaro, da kuma damuwa kan tada kayar baya daga kungiyar Boko Haram.

Shugaban hukumar zaben kasar mai zaman kanta, Parfessa Attahiru Jega ne ya fadi haka ga taron manema labarai. Yace "idan babu tabbaci kan kare lafiyar jami'an tsaro, da masu zabe, da masu sa ido kan zabe, da kayan zabe, muddin babu wannan, to rayuwar talaka maza da mata da matasa, da basu san hawa ba balle sauka, kuma damar a yi zabe sahihi cikin walwala, duk zasu kasance cikin hadari.

Mayakan Boko Haram da suke ikirarin musulunci suna rike da kasa mai fadi a arewa maso gabashin Najeriya, kuma kwararru suka ce gudanar da zabe a cikin lumana cikin wannan yanki zai yi wuya kwarai da gaske.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan yana neman wa'adi na biyu. Amma 'yan Najeriya masu yawa suna sukar lamarinsa da gwamnati da yake yiwa jagoranci kan abunda suka kira gazawar gwamnatnsa na shawo kan masu tsatsaurar ra'ayin.

Kasashen yammacin Afirka hudu sun bada sanarwar a farkon wunin jiya Asabar kan shirin zasu hada karfi su taimakawa makwabciyarsu Najeriya ta yaki Boko Haram.

Wakilai daga kasashen Benin,da kamaru, da Cadi, da Nijar, da Najeriya ne suka bayyana shirin ganin bayan Boko Haram, bayan sun tashi daga wani taron kwanaki uku da suka yi a kamaru.

Sai dai ba'a bayyana dalla dalla yadda za'a yi amfani da wannan runduna ba. Kuma ministan tsaro na kamaru Edgard Alain Mebe Ngo'o, ya ce yin bayani kan hakan, tamakar tona asirin soja ne.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:57 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG