Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015: Badakalar Dage Ranar Zabe


An yi zanga-zangar rashin yarda da jinkirta zabe, Fabrairu 6, 2015.
An yi zanga-zangar rashin yarda da jinkirta zabe, Fabrairu 6, 2015.

“Yanzu muka kammala ganawa da hukumar INEC kuma sam bamu amince da dage ranar zabe ba”, a cewar shugaban Jam’iyyar PDM Alhaji Bashir Yusuf.

A zahiri, jam’iyyun sun rabe gida biyu, masu mara baya ga PDP mai mulki na cewa a jinkirta, ko a dage zaben, ma’abota jam’iyyar adawa ta APC na cewa a’a, a gudanar da zaben.

Mataimakin shugaban jam’iyyar PDP Uche Sakondos, yace ba’a yiwa jam’iyyar shi adalci ba idan aka ce sunce a dage zabe, manufarsu shine a duba lamuran tsaro, a jinkirta zaben.

Abubakar Abdullahi Sokoto, shine Sakataren Jam’iyyar UPN ta Najeriya “jam’iyyata ta yarda a zakudar da zaben, sati daya, ko sati biyu. Kar a bada wannan sati shida.

Da Muryar Amurka ya tambayi Abubakar Sokoto ko basu yi la’akari da zargin da za’a yi musu ba, na cewa sun hada kai da jam’iyya mai mulki PDP, shine yace “a’a, kowa yazo ne, kana da jam’iyya, Jega ya baiwa kowa damar fadar ra’ayinsa”.

Dr. Sadiq Abubakar Gombe, shine Sakataren Jam’iyyar SDP dake watsi da dalilan jinkirta zaben.

“Jam’iyyu goma sha biyu daga cikinmu, mun tabbatar da cewa dole a yi zabe. Mun cewa INEC bamu yadda ba, kuma ba hurumin mu bane”, a cewar Dr. Gombe.

Yunusa Tanko dake jagorantar Zauren Bada Shawarwari ga Jam’iyyun Siyasa na nuna shugaban Hukumar Zabe, Farfesa Attahiru Jega shine yake da wuka da nama.

Farfesa Jega dai a halin yanzu ya shiga taro da Kwamishinonin Hukumar domin samar da matsaya. Za’a iya cewa komai na iya faruwa. Idan ba’a manta ba, a zaben shekara ta 2011 hukumar zaben ta taba dage zaben bayan an fara kada kuri’a.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:52 0:00
Shiga Kai Tsaye

Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG