Wannan yarjejeniya a kulla ta ne a gaban kungiyoyin addini, dana hukumar zabe, da kuma hukumar ‘yan sanda, da sauran makamantansu a matsayinsu na shaidu.
Kassim Gaidam, shine Kwamishin zabe a Jihar Gombe.
“Wannan mu muka shirya taro, amma wato kungiyoyin NAREC, wato hadakar kungiyoyin addinai sune suka shirya yarjejeniyar kuma ‘yan sayasan sun yarda sun sa hannu. Kumar yarda da sukayi suka saka hannu, wato kamar sun bi mataki da aka dauka a tarayya”.
Evangelist Musa ne shugaban Matasan Kiristoci na arewa maso gabashin Najeriya.
“Da farko, Gwamnan Gombe Ibrahim Hassan Dankwambo ya sa hannu akan wannan yarjejeniya, kuma ya tabbatar da cewa za’a yi zabe cikin lumana da gaskiya da adalci.”
Saleh Sha’aibu shine darekta na tarbiyya na Majalisar Kungiyoyin Matasa Musulmi ta Najeriya.
“Yanzu mu manufarmu shine samar da hanyoyi na daban na ilimantar da mutane.”
Rigigimu masu nasaba da siyasa na daga cikin manyan batutuwan dake ciwa jama’a tuwo a kwarya musamman ma ganin babban zaben Najeriya na karatowa.