Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015: Inda Goodluck Jonathan Ya Tsaya


Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a Maiduguri, Janairu 15, 2014.
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a Maiduguri, Janairu 15, 2014.

Shugaba mai ci a Najeriya, Goodluck Jonathan yana sake takarar neman shugabancin kasa a wa’adi biyu.

Shugaba mai ci a Najeriya, Goodluck Jonathan yana sake takarar neman shugabancin kasa a wa’adi biyu, sai dai akwai kalubale, musamman ta’addancin Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya.

Gazawar gwamnati wajen kawo karshen rigingimun Boko Haram ya jawowa Jonathan kalubale, batun da yasa wata kila mai adawa da shi, Janar Muhammadu Buhari ya lashe babban zaben 14 ga watan Fabrairu.

Rigingimu a arewa maso gabashin Najeriya ya kashe dubban mutane, sannan wasu 750,000 sun kaurace wa gidajensu.

A lokacin da yake yakin neman zabe a Najeriya, Mr. Jonathan ya dage akan cewa gwamnatinshi da sojoji zasu iya kawo karshe mayakan Boko Haram, da kuma dawo da zaman lafiya a arewa maso gabashin Najeriya bayan share shekaru 5 ana fada.

A arewacin Najeriya, jawaban Jonathan basu gimshi jama’a ba, sannan a wani karo an samu tashin bom jim kadan bayan fitarsa daga babban filin wasa dake garin Gombe.

Dama Mr. Jonathan baya samun goyon baya a arewacin Najeriya, tun bayan fara aikin shugabanci a watan Mayun 2010, lokacin da Shugaba Umaru Yar’adua ya rasu.

Marigayin shugaban Musulmi ne, kamar mafi yawancin mutanen arewacin kasar, yayin da Mr. Jonathan dan kudu ne, kuma yana bin addinin Kirista. Musulmai dake arewa na ganin cewa yanzu ne damarsu na hawa karagar mulki a kasar dake da addinai daban-daban.

Mr. Jonathan ya fusatar da jama’ar arewacin kasar a lokacin da ya yanke shawarar tsayawa takara a shekara ta 2011. Ya samu galaba akan Buhari saboda goyon baya da ya samu a kudancin kasar. Sai dai kazafce-kazafcen magudin zabe ya tayar da rigiginmu a arewacin kasar har yayi sanadiyar rayukan wasu mutane 800.

Gwamnatin Jonathan ta samu wasu nasarori, misali shine dakile yaduwar Ebola da aka yi a jihar Legas a shekarar da ta wuce. An kuma samu masalaha a yankin Niger Delta biyo bayan afuwa da gwamnatin Umaru Yar’adua ta baiwa mayaka dake kai hare-hare akan masana’antun man fetur.

Duk da tashe-tashen hankula a arewa maso gabashin Najeriya, Jam’iyyar PDP mai mulki ta kara zaben Mr. Jonathan mai shekaru 57 domin sake tsayawa takarar shugabancin kasa a watan da ya wuce.

Idan ya samu nasara, shugaban zai fuskanci kalubalen rashin isasshen kudaden tafiyar da harkokin kasa. Faduwar farashin man fetur a duk fadin duniya ya rage adadin kudaden shigar gwamnati, a kasar da tafi kowace kasa a nahiyar Afirka hako danyen man fetur.

Sai dai matsalar Boko Haram na iya zama babban matsalar da tafi cin tuwo a kwarya. Ta yiwu a samu sauki, saboda kungiyar Tarayyar Afirka ta goyi bayan aika sojoji 7,500 domin yakar ‘yan ta’addar. Sojojin Najeriya na daga cikin wannan runduna, tare da sojojin Chadi, Kamaru, Niger da kuma Benin.

XS
SM
MD
LG