Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015: Inda Muhammadu Buhari Ya Tsaya


Janar Muhammadu Buhari a Gombe Fabrairu 3, 2015.
Janar Muhammadu Buhari a Gombe Fabrairu 3, 2015.

Game da Muhammadu Buhari kuwa, zaben Najeriya dake karatowa shine babbar dama daya samu domin komawa kan karagar mulki da ya taba rikewa a shekarun 1980.

Game da Muhammadu Buhari kuwa, zaben Najeriya dake karatowa shine babbar dama daya samu domin komawa kan karagar mulki da ya taba rikewa a shekarun 1980, kuma yayi ta kokarin komawa tun wannan lokaci.

Buhari wanda yake Manjo Janar a rundunar sojan Najeriya a wannan lokaci, shine ya rike shugaban kasa ta mulkin soja a shekrun 1984 da 1985, biyo bayan juyin mulki da wasu sojoji suka yiwa Shehu Shagari wanda aka zaba ta hanyar demokradiyya.

Shima Buharin ya gamu da juyin mulki bayan watanni 20, amma ba kamar ragowar shuwagabannin soja ba, ya samu damar tsunduma cikin harkokin siyasa tun bayan komowar Najeriya mulkin demokradiyya tun 1999.

Wannan shekara, shine karo na hudu da Buhari yake sake neman shugabancin Najeriya. Ya zo na biyu sau uku a zaben shekarun baya, a cikin harda kayi da yasha daga Shugaba Goodluck Jonathan a shekara ta 2011.

A wannan shekara, masu lura da harkokin siyasa sun bayyana cewa Buhari zai iya yin nasara, musamman saboda gajiya da jama’a sukayi daga zub-da-jinin Boko Haram a arewa maso gabashin Najeriya. Buhar yace Mr. Jonathan ya gagara kawo karshen Boko Haram, kuma yayi alkawarin kawo karshen tashe-tashen hankulan idan aka zabe shi.

A karo na farko, Buhari ya samu goyon bayan hadakar jam’iyyun adawa. Jam’iyyu 9 ne suka hada gwiwa a shekarar da ta wuce, domin samar da All Progressives Congress, dake dauke da gwamnonin wasu manyan Jihohi, kuma suka zabi Buhari mai shekaru 72 domin ya tsaya takarar shugaban kasa.

Jam’iyyar APC na neman kawo karshen shekaru 16 da Jam’iyyar PDP ta Mr. Jonathan tayi tana mulki, lamarin da Buhari ya kira matsala ga Najeriya.

Tsohon Janar din ya kuma bayyana cewa zai mayar da hankali akan kawo karshen cin-hanci da rashawa, da kuma kara adadin tallafin da gwamnati take baiwa manoma da masana’antu domin bunkasa samun ayyukan yi.

Wani babban batu da ake fuskanta a karshen yakin neman zaben shine na dage ranar da zabe da wasu shuwagabannin siyasa da sojoji suke bada shawara saboda tashe-tashen hankulan arewa maso gabashin Najeriya. Buhar da jam’iyyar APC sun nace akan cewa ya kamata a gudanar da zabe, duk da cewa Boko Haram na kame wasu yankuna, kuma zasu hana dubban daruruwan mutane jefa kuri’a, lamarin da ka iya rage goyon bayan da Buhari yake samu.

Wannan dan takara shine yafi farin jini a arewacin Najeriya dake dauke da Musulmai, yankin da yafi samun goyon baya kennan a zaben shekara ta 2011.

XS
SM
MD
LG