A yayin da ranar babban zaben Nijeriya ke kara karatowa, Hukumar Zaben Nijeriya Mai Zaman Kanta (INEC) na cigaba da rarraba katunan zabe na dindindin, kodayake akwai korafe-korafen cewa abin na tafiyar hawainiya.
Abokin aikinmu Ibrahim Alfa Ahmed, wanda ya zanta da abokin aikinmu Bello Habib Galadanci wanda, ya ce duk da ya ke da wuya a ce kowa ya sami katin kafin ranar zabe, ga dukkan alamu hukumar ta zabe so ta ke ta abubuwa su kankama kafin cikar wa’adinta na ranar Lahadi. Ya ce Hukumar Zaben na kuma shirin ganawa da dukkannin jam’iyyun siyasar da ke Nijeriya a gobe Asabar don daddale al’amuran da su ka shafi makomar zaben kamar dai yadda ake ta takaddama. Ya ce har yanzu ana takaddama akan batun gudanar da zaben kamar yadda aka tsara. Amma ya ce Majalisar Kolin Nijeriya wadda ta yi taro jiya a Abuja, ta bai wa Hukumar Zaben Nijeriya damar yin abin da ta ga ya dace.
Ibrahim ya jaddada cewa Shugaban hukumar zaben, Furfesa Attahiru Jega ya nanata a wurin taron Majalisar Koli ta kasar cewa hukumar ta shirya sosai don gudanar da zaben. Ibrahim ya ce tuni hukumar ta fara kai kayan zaben zuwa jihohi, musamman ma takardun da ake dangwala yatsa akai ko “ballot papers.” Y ace kodayake hukumar zaben ta dage wajen ganin shiri ya kankama, ba ta gindaya wani adadi na shiri kafin zaben ba.