Mai nazarin harkokin mulki a kasashen Afrika farfesa Boube Na Mewa na jami’ar Diof dake Dakar, Senegal ya bayyana cewa, a ganin sa zaben Trump babban kuskure ne.
Shugaban Amurka mai barin gado Donald Trump ya yiwa mutane 73 afuwa tare da sauya hukunci wasu 70.
Yayin da mazauna lardin arewacin Najeriya ke fama da kalubalen tsaro da tattalin arziki da kuma rashin ayyukan yi, an kafa wata sabuwar kungiya da nufin farfado da martabar yankin na Arewa.
Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawallen Maradun ya mayar da martani kan zargin da jam'iyyar APC ta yi masa kan cewa shi ne ke daukar nauyin ta'addanci a shiyyar Arewa maso yammacin Najeriya.
Kungiyar Malaman Jami'o'in Najeriya ta ASUU ta bada sanarwar janye yajin aikin da ta fara a watan Maris da ya gabata.
Yayin da ‘yan kungiyoyin gwagwarmayar shugabanci na gari a Najeriya ke caccakar matakan wasu gwamnonin arewacin Najeriya na rufe makarantunsu, dalibai a kwalejin nazarin ilimin aikin malinta ta Sa’adatu Rimi a Kano sun gudanar da zanga-zanga.
Shugaban Ghana mai ci Nana Akufo-Addo da kuma John Mahama abokin adawarsa su ne su ka mamaye neman takarar zaben tsakanin 'yan takara 12.
'Yan Adawa sun kauracewa zaben majalisar dokokin Venezuela bayan da suka yi zargin an tafka magudi.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince ya gana da majalisar wakilai akan batun kalubalen tsaro da ake fuskanta a fadin kasar.
A ranar Litinin hukumomi a kasar Italiya sun ci tarar kamfanin Apple Euro miliyan 10, kimanin dala miliyan 12.
Wannan na zuwa ne yayin da Joe Biden ya damka wa mata sashen sadarwar fadar White House
Kasar Nijer da ke yammacin Afrika ta ayyana kwanaki 3 na zaman makoki a fadin kasar daga ranar Laraba 25 ga watan Nuwamba bayan da tsohon shugabanta Mamadou Tandja ya rasu ya na da shekara 82.
A ranar Litinin 23 ga watan Nuwamba ne wata babbar kotun tarayya a Abuja ta bada umarnin a tsare Sanata Ali Ndume saboda kin bayyana a gaban kotu da Abdulrasheed Maina ya yi bayan da Ndume ya tsaya mashi wajen bada belinsa.
Rundunar sojojin Isra’ila ta fada a yau Laraba cewa ta kai farmaki ta sama kan wasu wuraren Syria da Iran a Syria a matsayin maida martini kan ajiye ababen fashewa a bakin iyakar kasar da ke yankin tsaunin Golan a cewar Isra’ila.
Tabarbarewar harkokin tsaro shine kan gaba a jerin batutuwan da ke damun kasar Burkina Faso, inda masu kada kuri’a zasu nufi rumfunan zabe ranar Lahadi 22 ga watan nan don zaben shugaban kasa da ‘yan majalisar dokokin kasar.
Shugaban ya yi ikirarin cewa kalaman Chris Krebs kan gamsuwa da sakamakon zaben 2020 ba daidai ba ne.
Yayin da kwamitocin binciken zanga-zangar ENDSARS da wasu gwamnonin Najeriya suka kafa ke ci gaba da sauraron bahasi daga jama’a, masu kula da al’amura suna tsokaci akan cancanta ko rashin cancantar kafa kwamitocin, da kuma hasashe akan tasirin rahotannin da zasu mika wa gwamnati.
Shugaban kwamitin wasannin Olympics na kasa-da-kasa ya ce kwamitin zai dauki matakai don tabbatar da cewa an ba dukkan 'yan wasa da wadanda zasu halarci gasar wasannin riga kafin COVID-19 a watan Yulin shekarar 2021.
Domin Kari