Ta shafinsa na twitter Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da korar Krebs, daraktan cibiyar tsaron yanar gizo ta Amurka, saboda bayanan da Krebs din ya yi a kwanan nan game da zaben kasar.
Krebs ya sha karyata zarge-zargen magudin kuri’u a ‘yan makonnin da suka gabata, ya rubuta a shafinsa na twitter cewa, “game da zarge-zargen an yi ba daidai ba a tsarin zaben, kwararru masu kula da tsaron kuri’u 59 dukkansu sun yarda cewa, a kowanne zargi da muke da masaniya akai, ko dai babu wata kwakkwarar hujja da aka gabatar ko kuma dai babu makama a zargi-zargen.
A jiya Talata ne Trump ya rubuta a shafinsa na twitter cewa bayanan Krebs “ko kadan ba daidai ba ne” ya na mai zargin an tafka magudi sosai a zaben.
"A saboda haka, ba tare da bata lokaci ba, an sauke Chris Krebs daga mukamin daraktan cibiyar tsaron yanar gizo ta Amurka, a cewar sakon shugaban."