Jihohin Lagos, Rivers, Kaduna, Plateau, Adamawa, Bauchi da kuma Edo na daga cikin wadanda suka kafa kwamitin binciken domin bibiyar zarge-zargen da masu zanga-zangar neman a soke rundunar ‘yan sandan SARS su ke yi da kuma tarzomar lalata dukiyar gwamnati a wasu daga cikin jihohin Najeriya.
Babban makasudin kafa kwamitin dai bai wuce kokarin da mahukuntan Najeriya ke yi na tabbatar da adalci game da wannan batu, sai dai masu nazari akan lamuran yau da kullum sun zo da wani hanzari game da wannan batu.
Dr. Sa’idu Ahmad Dukawa, malami ne a tsangayar nazarin Ilimin gudanar da Mulki ta Jami’ar Bayero da ke Kano, ya ce in har hukumomin Najeriya suna bin diddigin zarge-zargen, tare da hukunta duk wanda kotu ta tabbatar ya aikata laifin cin zarafi, to hakan zai magance matsalar.
Fadar shugaban Najeriya ce dai ta bai wa gwamnoni umarnin kafa kwamitocin sauraron bahasi akan korafin ayyukan jami’an ‘yan sandan SARS, amma Alhaji Abdulkarim Dayyabu kwamandan rundunar gwagwarmayar wanzar da adalci a Najeriya ya ce ya kamata shugaban Najeriya ya kafa kwamiti mai karfin shari’a wanda zai tabbatar da an yi bincike da hukunta masu laifi.
Watakila irin wannan nazari ne ya sa wasu daga cikin gwamnonin na Najeriya ba su damu da kafa kwamitin binciken na ENDSARS ba, musamman la’akari da cewa, jami’an rundunar SARS sun taka rawar ga ni a jihohi irin su Borno, da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Ga Mahmud Ibrahim Kwari da cikakken rahoton: