Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Biden Ya Kuduri Aniyar Yaki Da COVID-19 Sosai


Shugaba Joe Biden mai jiran gado ya ce, zai tashi tsaye sosai wajen yaki da annobar COVID-19, cikin matakan da zai dauka har da kara yawan riga kafin da ake yi wa mutane, yayin da gwamnatin shugaba Donald Trump ke yin burus da sukar da ake yi mata game da matakan da ta dauka na yaki da cutar wadda ta kashe kusan mutane 339,000 a Amurka.

An dan sami ci gaba kadan a cikin ‘yan kwanakin nan a kasar a adadin masu kamuwa da cutar ba kamar yadda aka gani ba watannin 2 da suka gabata, amma har yanzu ana samun kari kan kusan mutun 180,000 masu kamuwa da cutar da ake samu a duk rana kuma jami’an lafiya sun yi gargadin cewa, tafiye-tafiyen lokacin hutun Kirsimeti da sabuwar shekara ka iya kara yawan masu kamuwa da cutar.

Yayin da ya rage kasa da wata guda ya karbi mulki, a jiya Talata Biden ya fada bayan wata ganawa da kwararru cewa, gwamnatin Trump ta na yin tafiyar hawainiya a kokarinta na yi wa mutane riga kafin.

Biden ya kuduri aniyar za a yiwa mutane miliyan 100 riga kafin a kwanaki 100 na farkon mulkinsa.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG