Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Yiwa Mutane 73 Afuwa Kafin Bankwana da Kujerar Mulki


Shugaban Amurka mai barin gado Donald Trump ya yiwa mutane 73 afuwa tare da sauya hukunci wasu 70.

An bayyana sunayen wadanda shugaban ya gatanta ne a sanarwar da aka fitar fadar White House da sanyin safiyar yau Laraba, sa’o’i kadan kafin wa’adin mulkinsa ya kare.

Afuwar dai ta hada da tsohon shugaban yakin neman zaben Trump, kuma babban mai bashi shawara, Steven Bannon, wanda aka tuhuma da damfarar dubban mutane da suka bada kudaden su domin aikin gina katanga a tsakanin iyakar kudancin Amurka.

Babban mai baiwa Trump shawara, Steven Bannon
Babban mai baiwa Trump shawara, Steven Bannon

Masu gabatar da kara sun zargi Bannon da yin amfani da sama da dala miliyan daya don biyan jami’an yakin neman zaben su da yiwa kansa hidima.

Trump ya sauya hukunci da aka yankewa tsohon magajin garin Detroit, Kwame Kilpatrick, wanda ya ke zaman gidan yari na sama da shekara 20 saboda amfani da mukaminsa a matsayin zababben shugaba da aka kama da laifin cin hanci da rashawa.

mawaki Lil Wayne
mawaki Lil Wayne

Haka kuma shugaban kasar ya yi afuwa ga Dwayne Carter Jr., mawakin gambarar nan da aka fi sani da Lil Wayne wanda ya amsa laifin mallakar makamai.

Sai dai kamar yadda aka yi tunani, Trump bai yiwa kansa ko iyalinsa ko kuma fitattaccen lauyansa kuma amininsa Rudy giuliani.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG