Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Kammala Wa'adin Mulkinsa


A yau Laraba Donald Trump ya kammala wa’adin mulkinsa na shekara 4 a matsayin shugaban Amurka ya kuma bar fadar White House a jirgin shugaban kasa na Air Force One zuwa jihar Florida da ke kudancin Amurka.

An yi masa kasaitaccen bikin ban kwana, tare da faretin sojoji da harba bindiga har sau 21.

Trump yayin jawabin Bankawana
Trump yayin jawabin Bankawana

A daidai lokacin da jirgin zai sauka, za’a rantsar da Joe Biden na jam’iyyar Democrat a matsayin sabon shugaban kasa, yayin da Trump ya saba al’ada ta shekaru da dama na kin halartar bikin rantsuwar.

Shugaba Trump ya bar ofis ya kuma zama shugaban kasa na farko a tarihin Amurka da aka tsige shi sau biyu, yayinda Majalisar Dattawa ta ke shirin fara sauraran shari’a kan tuhume-tuhumen tunzura magoya bayansa su mamaye ginin Majalisar Dokokin Amurka na Capitol makonni biyu da suka gabata da zai tabbatar da tsige shi a hukumance matakin da zai hana shi sake rike mukamin siyasa a Amurka da kuma cin moriyar duk wata dama da ake ba tsofaffin shugabannin kasa.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG