Sanata Ali Ndume ya shafe kwanaki biyu a tsare duk da cewa ya daukaka kara ta hannun lauyan da ke kare shi don neman beli tun ranar Litinin da aka tsare shi a gidan yarin Kuje da ke birnin tarayyar Abuja saboda kauracewa zaman kotu da tsohon shugaban kwamitin asusun ‘yan fansho Abdulrasheed Maina ya yi, wanda ake zargi da wawure kudadden al’umma.
Dakta Sa’idu Dukawa, mai fashin baki a kan al’amuran yau da kullum ya bayyana ra’ayinsa game da tsare Ndume, inda ya ce kundin tsarin dokar Najeriya ya tanadi a hukunta duk wanda ya karya doka duk girmansa ko matsayainsa.
Majiyoyi daga babbar kotun tarayya da hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa sun tabbatar da cewa Ndume ya gabatar da dalilai 12 na daukaka kara amma kotu ta yi watsi da su, a ta bakin tawagar lauyoyin sa da Marcel Oru ke jagoranta .
Dan uwan Maina, Mallam Aliyu Maina, ya yi kira ga dan uwan nasa ya mika kansa ga hukuma ganin yadda Sanata Ndume ya sadaukar da kansa.
A wani bangare kuwa, kungiyar MASSOB mai fafutukar ganin an raba Najeriya tare da kafa kasar Biafra, ta yi gargadin cewa kasar Igbo ba zata zura ido a kama Sanata Enyinnaya Abaribe ba wanda ya tsaya wa shugaban kungiyar IPOB Nnamdi kanu, ta na mai cewa akwai bambanci akan batutuwan Abaribe da Ndume.
A shekarar 2010 ne tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya nada Abdulrasheed Maina wanda ake zargi da wawure kudadden fansho da aka kiyasta yawansu ya kai naira bilyan 100, a lokacin da ya ke rike da mukamin shugaban kwamitin da zai kawo sauyi a sha’anin ‘yan fansho domin yin gyara da ake bukata.
Ga Halima Abdulra’uf da cikakken rahoton: