An ci tarar kamfanin na Apple ne akan ikirarin da ya yi game da cewa, ruwa baya lalata wayar salula ta iPhones.
Hukumomin sun ce, ikirarin kamfanin na Apple game da tsawon lokacin da wayoyin iphone za su iya kasancewa a cikin ruwa ba tare da sun lalace ba, na yiwuwa ne kawai a yanayi na matakin gwajin da aka yi dakunan bincike.
Sun kuma kara da cewa, kariyar da kamfanin na Apple ya bayar ga wadanda wayoyinsu suka lalace sanadiyar fadawa a a ruwa ta cutura samu.
Rahotan mujallar kasuwanci ta Business Insider ya nuna cewa, kamfanin na Apple ya yi ikirarin cewa, nau'ukan wayar salula na iphone daban-daban ba sa lalacewa idan aka saka su a ruwa mai zurfin kafa 3 zuwa 13, har na tsawon minti 30.