Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Zaben Shugaban Kasa Da Na 'Yan Majalisu A Ghana


Masu kada kuri'a a Ghana.
Masu kada kuri'a a Ghana.

Shugaban Ghana mai ci Nana Akufo-Addo da kuma John Mahama abokin adawarsa su ne su ka mamaye neman takarar zaben tsakanin 'yan takara 12.

An fara kada kuri'a a kasar Ghana da ke yankin yammacin Afirka, inda ake zaben shugaban kasa da neman kujerun majalisar dokoki 275.

Duk da cewa ‘yan takara 12 ne su ke neman shugabancin kasar, amma ana kallon fafatawar tamkar ta mutum biyu ce, tsakanin shugaba mai ci Nana Akufo-Addo na jam’iyyar New Patriot Party da tsohon shugaban Ghana John Mahama, shugaban jam’iyyar adawa ta National Democratic Congress.

Wannan ce takara ta uku tsakanin su biyun tun daga shekarar 2012, a karon farko Mahama ya kayar da Akufo-Addo, sannan daga baya Akufo-Addo ya samu nasara a shekarar 2016.

Mata uku ne cikin ‘yan takara 11 da ke kalubalantar Akufo-Addo, amma an fi mai da hankali kan Jane Naana Opoku-Agyemang, tsohuwar ministar ilimin Ghana wacce ke takarar mukamin mataimakiyar Mahama, abinda ya ba ta dama ta zama mace ta farko da ta samu tikitin takara a wata babbar jam’iyyar siyasa a Ghana.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG