Gwamnan jihar Zamfara ya ce an kitsa wannan zargin ne don batanci ga gwnmnatin jihar ganin cewa lokacin da ya karbi mulki jihar na aiki sosai, domin a wancan lokacin ana samun labaran kashe-kashe a kullum a jihar.
Amma bayan karbar mulki gwamnan ya ce labarin ya canza domin hatta ‘yan kudancin Najeriya na ganjn cewa Zamfara na da arzikin da za a raba a kasa ba labaran kashe-kashe ba, don haka zargin da ake masa shiririta ne a cewarsa, an fi samun ayyukan ta’addanci a zamanin da APC ke mulki a jihar, al'amarin da gwamnatinsa ke kokarin shawo kan matsalar.
Da ya ke amsa tambaya akan ko me ya sa in an yi garkuwa da mutane a jihohi makwabta ake samun mafaka a jihar? gwamnan ya ce Zamfara kasa ce ta Fulani. Lokacin da ya zauna sulhu da Fulani ‘yan bindiga sun yi korafin a baya su na zamansu lafiya amma sai ‘yan sa kai suka dinga kashesu, dalili kenan da ya sa ya soke kungiyoyin sa kai.
Gwamnan ya kuma ce fulani su ma ‘yan kasa ne kuma su na da hakki akan gwamnatocin su don haka zai yi duk mai yiwuwa don tabbatar da kare rayukan talakawansa.
Karin bayani akan Bello Muhammad Matawalle, jihar Zamfara, APC, da Fulani.