Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Isra’ila Sun Kai Wa Wasu Wuraren Syria Da Iran Farmaki Ta Sama


Rundunar sojojin Isra’ila ta fada a yau Laraba cewa ta kai farmaki ta sama kan wasu wuraren Syria da Iran a Syria a matsayin maida martini kan ajiye ababen fashewa a bakin iyakar kasar da ke yankin tsaunin Golan a cewar Isra’ila.

Kafar yada labaran gwamnatin Syria ta SANA ta ambaci wata majiyar soja na cewa farmakin ta sama ya yi sanadiyyar kisan sojoji 3 tare da jikkata wani. Ta kira hare-haren “tsokana daga Isra’ila.”

A wata sanarwa da Isra’ila ta fidda ta zargi wata tawagar sojojin Syria a karkashin jagorancin dakarun Iran da girke ababen fashewa. Ta ce harin na ramuwar gayya ya auna rumbunan ajiya, da harabar sansanonin soja da kuma makaman kariyar Syria ne.

“A shirye muke mu maida martini kan duk wani kutse a Syria,” a cewar sanarwar sojojin.

Iran kasar huldar shugaban Syria Bashar al-Assad ce kuma ta tura sojoji masu bada mashawara da mayakan kawance don su taimaka wa dakarun Syria a lokacin yakin basasar kasar.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG