Tun a farkon watan nan, gwamnatin Nijar ta sanar cewa akwai yiyuwar ‘yan ta’adda za su kwatanta kai hari a birnin Yamai mafarin abin da ya sa jami’an tsaro suka kaddamar da wani binciken ababen hawa.
A birnin Yamai kuma kungiyoyin addinin Islama na ci gaba da kiraye-kirayen kwantar da hankali.
A jamhuriyar Nijar wasu ‘yan majalisar kasashen Afirka sun fara gudanar da wani taro a karkashin majalisar dinkin duniya da hadin guiwar kungiyar majalisun kasashen duniya UIP, domin nazarin gudunmawar da majalisu ke iya bayarwa kan yaki da ta’addanci.
Lura da yadda dalilan siyasa ke zama wata hanyar haddasa rarrabuwar kawunan jama’a a yau a wannan nahiya, ya sa kungiyar Les Nigeriens sont des cousins daukar matakan kaucewa fadawa irin wannan tarko.
Jerin gwanon 'yan Shi'ah sun gudanar da muzahara a Birnin Yamai.
Mazauna yankunan Yamai da Dosso da Tilabery sun fada cikin mawuyacin halin rayuwa a sakamakon daukewar wutar lantarki da ake huskanta yau kimanin kwanaki uku, matsalar da kamfanin wutar lantarki Nigelec ya danganta da faduwar wasu karafunan tangarafu tsakanin birnin Kebbi da birnin Gaure.
Daruruwan mutane maza da mata ‘yan asalin yankin Diffa mazaunan birnin Yamai ne suka hallara a taron da kungiyarsu ta kira da nufin tattaunawa kan matakan tsaro domin gudanar da ayyukansu ba tare da wata fargaba ba.
Ganin yadda aka shiga bayyana shakku kan yiwuwar hukumar zaben Janhuriyar Nijar ta kintsa kafin lokacin zaben 2021, hukumar ta yi maza ta ce idan ma akwai matsala to ba ita ce sanadi ba; kamfanin kasar Faransa da aka ba shi aikin samar da kundin rajista ne, kamfanin kuwa ya ce a'a.
A Jamhuriyar Nijer, cinkoson jama’a a manyan birane wanda ya samo asali daga karuwar yawan al’umar kasar ya haddasa karancin ruwan sha, lamarin da ya sa gwamnatiin kasar ta soma daukar matakai domin magance wannan matsalar.
Fayfan bidiyon wanda hukumomin Nijar suka haramta wallafa shi ta kowace irin kafa na dauke ne da wani sako wanda a cikinsa Hama Amadou ke nuna jin takaici akan abin da ya kira gazawar gwamnatin Nijar wajen shayo kan matsalar tsaro.
Shugaban kasar Nijar Issouhou Mahamadou ya tattara manyan hafsoshin soja da jakadun Amurka da Faransa, a yinkurinsa na sake damara don inganta tsaron kasar, mako guda bayan mummunan harin da ya hallaka sojojin Nijar.
Ofishin jakadancin Amurka a jamhuriyar Nijar ya shirya liyafar bude baki ma Musulmin kasar, a albarkacin watan Ramadan.
Shugaban kasar Nijer Issouhou Mahamadou ya jaddada aniyar ci gaba da jajircewa domin murkushe kungiyoyin ta’addancin dake tada zaune tsaye a kasar da makwaftan ta.
A caigaba da fuskantar kalubalen tsaro da ake yi a yankin Sahel na Afirka, sojoji masu tarin yawa sun halaka, bayan da wasu ‘yan bindiga suka bude wuta a Jamhuriyar Nijer.
A jamhuriyar Nijer yau aka fara Zaman makoki na kwanaki uku da nufin nuna alhinin rasuwar mutane sama da hamsin, da suka Kone kurmus.
Gwamnatin ta dauki matakin ne don ganin cewa mabiya addinai mabambanta sun ci gaba da mutunta juna.
Yayin da ake cigaba da samun matsalolin tsaro a Janhuriyar Nijar, wata gamayya ta jam'iyyun 'yan adawa ta yi gangami a birnin Yamai, inda ta bukaci gwamnati ta tashi haikan wajen tabbatar da tsaro da inganta yanayin rayuwa.
Domin Kari