Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘Yan Majalisar Kasashen Afirka Sun Gudanar Da Taron Yaki Da Ta'addanci


Taron Majslisar Kasashen Afrika a Nijar
Taron Majslisar Kasashen Afrika a Nijar

A jamhuriyar Nijar wasu ‘yan majalisar kasashen Afirka sun fara gudanar da wani taro a karkashin majalisar dinkin duniya da hadin guiwar kungiyar majalisun kasashen duniya UIP, domin nazarin gudunmawar da majalisu ke iya bayarwa kan yaki da ta’addanci.

Sanin babban kusancin dake tsakanin talakawa da masu wakilancin al’umma a majalisun dokoki, ya sa majalisar dinkin duniya da kungiyar hadin kan majlisun kasashen duniya UIP shirya wannan taro na hadin guiwa da majalisar dokokin jamhuriyar Nijar, domin samun hanyoyi da matakan cimma nasara kan matsalolin ta’addanci inji dan majalisar dokokin kungiyar CEDEAO, Boukary Sani Zilly.

samun hadin kan majalisun dokoki wajen daukar wasu mahimman matakai a kasashen dimokradiyya wani abu ne da ya zamar wa gwamnatoci tilas, saboda haka mataimakin shugaban majalisar dokokin Nijar, Iro Sani ke cewa, majalisu na da rawar takawa a yaki da ta’addanci.

Zurfafa bincike domin gano ainihin tushen makaman da ‘yan ta’adda ke amfani da su na daga cikin hanyoyin da ake ganin zasu taimaka a murkushe aiyukan ta’addancin da suka addabi jama’a.

Kasashen Algeria, Burkina Faso, Cameroun, Cote d’ivoire, Djibouti, Mali, Marocco, Nijar, Senegal da Chad ne, suka halartar wannan taron da za'a kammala gobe juma’a, yayinda Italia da kenya da Autriche ke wakiltar kwamitin tuntuba na kungiyar UIP a matsayin ‘yan kallo.

A saurari cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

Facebook Forum

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG